Akwai Yiwuwar Girgizar Kasa a Nijeriya- Hukumar NASRDA

Daga Nazleey Muhammad

Hukumar binciken sararin samaniya wato NASRDA ta bayyana cewa akwai yiwuwa girgizar kasa a tarayyar Nijeriya.
A inda ta gargadi al'umma musamman al'ummar jihohin da ake zaton girgizar kasar zai auku akan da su sanya kula.

Babban Daraktan hukumar wato Farfesa Seidu Mohammed ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja. An bayyana jihohi hudu ciki harda birnin tarayya Abuja a matsayin Biranen da wannan lamari zai shafa. Inda girgizar kasar zai shafa sun hada da: Mpape a birnin tarayya, Abuja, sai garin Kwoi a jihar Kaduna da kuma Ijebu-Ode a jihar Ogun, sannan sai Shaki a jihar Oyo da kuma Igbogene a jihar Bayelsa.

Ya ce idan har ana son kaucewa wadannan dole ne a dauki matakan bincike wanda suka dace domin ganin an magance irin wadannan matsaloli.

MUJALLARGWAGWARMAYA
28092018

Post a Comment

0 Comments