Shafin yada labarai na Afaq ya bayar da rahoton cewa, kwamitoci da
kungiyoyin Musulmi a Yemen sun fitar da bayani da ke yin kira zuwa ga taimakon
al’ummar Falastinu.
Bayanan sun mayar da hankali ne kan ci gaba da mamayar yankunan
Falastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi, tare da jaddada
wajibcin daukar matakai na taka ma Isra’ila birki kan hakan.
Haka nan kuma bayanan sun nuna takaici kan yadda wasu daga cikin
kasashen Musulmi da na Larabawa suka zama abokan kawance ga haramtacciyar kasar
Isra’ila wajen kitsa makirci akan al’ummar Falastinu kamar yadda shafi Abna24
suka labarto.
Daga karshe Musulmin na Yemen sun jaddada wajibcin hadin kai
tsakanin dukkanin kasashen Larabawa da na Musulmi kan batun Falastinu, da kuma
daukar matakai na bai domin taimakon Falastinawa.
0 Comments