Daga Saifullahi M. Kabir
Ranar 12 ga watan Satumba, rana ce mai muhimmanci
da Harkar Musulunci a Nijeriya ta ware musamman don tunawa da waki’ar janaral
Dogo da bindiga (Sani Abacha), domin kuwa a irin wannan ranar ta 12 ga Satumbar
1996 ne Janar Abacha ya daura dukkan damararsa na ganin ya kawar da Harkar
Musulunci da Jagoranta, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
A wancan lokacin, a ranar Alhamis 12 ga Disambar
1996 da sanyin safiyar wannan ranar, misalin karfe 6 na safiya, yan sanda da
muggan makamansu sun zo gidan Jagora, Shaikh Zakzaky ne a cewarsu sun zo ne don
su gabatar da bincike a gidansa, inda suka shiga duba duk inda suke bukata ba
su samu ko da wuka ba da sunan makami, don haka sai suka fito fili suka nunawa
su Malam cewa lallai sun zo su tafi da shi ne kawai. Ba wata-wata Jagora yace a
je, ya shirya hakan, ya kuma yi nasiha ga yan uwan da suke tare da shi, sannan
suka tafi da shi.
Wannan yasa washe gari Juma’a (13/9/1996) aka
shirya gagarumar Muzaharori don bayyanawa duniya halin da ake ciki da kuma nuna
rashin yarda da kama Shaikh Zakzaky da Janar Abacha ya yi, wanda aka gabatar da
gagarumar Muzahara a garin Zariya, muzaharar da dubun-dubatar ‘yan uwa suka
halarta, sai ya zamana an turo ‘yan sanda sun budewa Muzaharar wuta, ta kai ma
ga an samu ruwan Shahidai. Domin kuwa wannan ne karon farko da a take aka samu
‘yan uwa akalla 15 da suka yi Shahada nan take a tarihin Harkar Musulunci.
An faro Muzaharar ne daga masallacin Juma’a na
sabon gari, aka miko ta kan titin PZ aka nufo cikin garin Zariya, a yayin da
Shaikh Muhammad Turi ke gaban Muzaharar yana jagorantar ‘yan uwa suna tafe
cikin tsari da nizami. A daidai lokacin da aka iso wajen shatale-talen da ke
gaban kofar doka, sai aka ga ‘yan sandan mobayil sun yi layi sun tare kofar
shiga Zariya cikin shirin bude wuta.
Ganin haka sai ‘yan uwa suka kara chaji, suka ninka
kabarbarin da suke yi tare da Hailala, suka tunkari ‘yan sandan nan, ai kuwa
‘yan Sandan suka fara budewa ‘yan uwa wutan kan mai uwa da wabi, wasu suna
harba tiyagas, wasu suna harba bindiga akan ‘yan uwa. Amma sai ya zama ‘yan uwa
sun samu sabati, ana harbi wasu na fadi kasa amma ‘yan uwa suna kara dannowa,
har zuwa lokacin da ‘yan Sandar nan suka ga harsashinsu zai kare, nan suka ari
na kare ta hanyar Jos.
A yayin da suke harbin, yan uwa na cidadowa,
Shaheed Turi Allah ya kara masa rahama da jinkai, yana karawa ‘yan uwa chaji,
saboda tsayawar da ya yi da dakewarsa a matsayinsa na jagoran Muzaharar yasa
‘yan uwa ma suka dake, sai ya zamana ‘yan can baya ma ba su san an yi harbi ba,
sai dai wasu da suka kariso wajen kofar Doka suka ga jini a kasa, aka ce musu
ai an bude wuta ne, yayin da wasu kuma sun dai ji kamar tiyagas amma ba su
tabbatar ba, wasu kuwa sai da aka je wajen rufewa suka ga ana daddaga mutane
aka ce musu ai an samu Shahidai.
An ayyana cewa za a rufe Muzaharar ne a Babban
Dodo, hakan kuwa aka yi, an iya raka ‘yan Sandan a na-kare, aka wuce aka shiga
Zariya aka yi burki a filin na Babban Dodo, inda su ma wadanda aka harba aka
kwashe su zuwa can. Bayan da ‘yan uwa suka hadu ne, sai aka gabatar da jawabi
akan dalilin wannan Muzaharar, aka kuma sanar da ‘yan uwa irin ta’addancin da
‘yan sanda suka yin a bude wuta akan ‘yan uwa masu Muzaharar lumana, inda a nan
ne da yawan ‘yan uwa suka ma san cewa ashe ‘yan Sanda sun bude wuta. Kun san a
wancan lokacin, shekaru 21 kenan baya, ba kafafen sadarwa kamar yanzu, kuma
‘yan uwa sun halarci Muzaharar sosai.
A Babban Dodo ne aka daddago gawarwakin Shahidan da
aka harba, inda nan take wajen ya rude da Kabbarori. Ya zama Shaikh Muhammad
Turi ne ya jagoranci sallar Janazarsu. Amincin Allah ya kara tabbata a gare su.
‘Yan uwan da suka samu rabon Shahada a wannan
Muzaharar ta rashin yarda da kama Malam sune, kamar yadda yake a takardar da
Shaikh Muhammad Turi ya sakawa hannu a ranar Larabar bayan waki’ar 18/9/1996
sune:
1- Shaheed Abdullahi Musa– Shekaru 22
2- Shaheed Yusuf Musa T/Jukum – Shekaru 20
3- Shaheed Usman Sulaiman Kwangila – Shekaru 30
4- Shaheed Usman Ibrahim Waziri Samaru – Shekaru 24
5- Shaheed Salisu Abdullahi Gabari – Shekaru 23
6- Shaheed Alhasan Badamasi D/Tagwai – Shekaru 40
7- Shaheed Musa Muhammad Dumbi
8- Shaheed Jabu Muhyiddeen Kano.
9- Shaheed Ishak Salihu Mahuta
10- Shaheed Ashiru Yusuf Mahuta – Shekaru 21
11- Shaheed Muhammad Auwal T/Wada Zariya.
12- Shaheed Aliyu Alhaji Sadau
13- Shaheed Abubakar Rabi’u – Dan shekara biyu da rabi.
14- Shaheed Nuhu Adamu Dokan Mai jaki.
15- Shaheed Isa Musa Muciya.
2- Shaheed Yusuf Musa T/Jukum – Shekaru 20
3- Shaheed Usman Sulaiman Kwangila – Shekaru 30
4- Shaheed Usman Ibrahim Waziri Samaru – Shekaru 24
5- Shaheed Salisu Abdullahi Gabari – Shekaru 23
6- Shaheed Alhasan Badamasi D/Tagwai – Shekaru 40
7- Shaheed Musa Muhammad Dumbi
8- Shaheed Jabu Muhyiddeen Kano.
9- Shaheed Ishak Salihu Mahuta
10- Shaheed Ashiru Yusuf Mahuta – Shekaru 21
11- Shaheed Muhammad Auwal T/Wada Zariya.
12- Shaheed Aliyu Alhaji Sadau
13- Shaheed Abubakar Rabi’u – Dan shekara biyu da rabi.
14- Shaheed Nuhu Adamu Dokan Mai jaki.
15- Shaheed Isa Musa Muciya.
Wadannan sune Shahidan da aka samu nan take a
wannan lokacin da ‘yan sanda suka afkawa Muzaharar KAMUN MALAM ZALUNCI NE da
aka yi a Zariya ranar 13 ga Satumbar 1996. Wanda kuma Larabar da ta biyo bayan
wannan, an kuma yin wata Muzaharar a Kaduna, inda ‘yan Sanda suka kara bude
wuta, aka samu Shahidai. Wanda Insha Allah labarinsa yana tafe.
Abu mai muhimmanci shine, mu iya sani cewa ba tun
yau bane azzaluman mahukuntar kasar Nijeriya suke shekar da jininmu, ta yadda
abin kuma ba zai taba kawo karshe ba har zuwa lokacin da zai zama da taimakon
Allah mun kaisu kasa! Mun kafa tutar Musulunci a kasar nan, ya zama ba za a yi
komai ba face ance Allah da AnnabinSa yace.
Matasa, mu duba mu gani, mafiya yawan Shahidan can
da aka lissafo matasa ne ‘yan kasa da shekaru 30. Hakika mu ne muke da dama
cikakkiya na nemawa kai Shahada wajen taimakon bawan Allah din nan akan kiran
da yake yi na a komawa addinin Allah. Matakin farko shine mu gyara kanmu, mu
kyautata alakarmu da Allah (T), a sannan sai mu ce; Karyar Bindigar azzalumi ta
tsoratamu ko ta sa mu ja da baya. Muce, Mune mataimakan Shaikh Zakzaky, kuma
rayuwarmu ta zama fansa gare shi. A wannan lokacin da zai zama ba mai tsoron
mutuwa a cikinmu, a sannan ne daukakarmu za ta bayyana, taimakon Allah zai zo
mana, a wannan lokacin rashin yawanmu da rashin karfinmu ba za su hana
azzalumai su firgita ba.
Dazu nake tambayar wani Malamina cewa, wane irin
yawa ne Muzaharar da aka yi bayan kama Malam a 1996 ta yi da har ya zama mafiya
yawan mahalartan ba su san an bude wuta a Muzaharar an samu Shahidai masu yawa
ba sai da aka zo Babban Dodo wajen rufewa? Don ina iya tunawa, an je da ni
Muzaharar ina karami, amma ko ni ban san an yi wani harbi ba sai da muka je
Babban Dodo muka ji ana cewa an samu Shahidai a kofar doka. Sai yake ce min ai
an cika sosai ne ta yadda yayin da ake harbin a Kofar doka, wasu na sahun
Muzaharar suna can inda aka taso. Don haka jinin da ke kan kwalta ma ‘yan uwa
sun take shi kafin zuwan na baya.
Wannan a wancan lokacin kenan, shekaru kimanin 22
da suka gabata, sannan kuma a Mulkin Soji wanda shi dama kai tsaye an san
mulkin kama-karya da danniya suke yi. Ashe da za mu zama masu sadaukar da
rayukanmu da cire tsoron mutuwa za mu hadu a Muzaharar mutanen da ko da jami’an
tsaro aka turo ba za su iya hanamu abin da muke yi ba. Abin takaici ne yadda
akan kira Muzahara ya zama in an samu mutane masu yawa ne a samu mutum dubu
daya, wanda a shekaru 21 da suka wuce ‘yan uwa sama da dubu hamsin sun iya fita
Muzaharar A SAKI ZAKZAKY a rana guda. Tare da an shekar da jininsu a Zariya
ranar Juma’a a Zariya, bai hana su kuma fita ranar Laraba a Kaduna ba! Ina
‘ya’yan wadannan jajirtattun ‘yan uwan da a wancan lokacin su ne matasan
Harkar? Kulenmu!
A karshe ina cewa; Yadda Abacha ya yi Mushe ya bar
Malam Zakzaky, haka Buhari zai zama mushe ya bar Malam Zakzaky nan ba da jimawa
ba, kuma ba makawa sai Allah ya saka mana akan duk mai hanu a zaluntarmu. Insha
Allah. Kuma muna fadawa hukumar kasar nan ma’abociyar bijirewa dokokin Allah da
ma dokokinta na karan kanta da shaidan ya tsara mata, ta gaggauta sakin
Jagoranmu Shaikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba. Allah ne Majibincinmu,
kuma ba ku da majibinci face Shaidan tsinanne!
-MujallarGwagwarmaya
13092018
0 Comments