Daga Abubakar Musa
An harbe mutumin da a 2023 ya kona Alkur’ani da yammacin ranar Laraba a gidansa da ke Stockholm, Sweden, kamar yadda kafofin watsa labarun cikin gida suka ruwaito a cewar kafar watsa labaru ta Politico.
Kamar yadda kafar ta Politico ta bayyana, Salwan Momika tun da farko an shirya za a gurfanar da shi ne domin ya fuskanci shari'a sakamakon kalaman tunzura jama'a a yau Alhamis.
Wani Alkali da ke kotun gundumar Stockholm, Goron Lundhal, ya tabbatar da cewa an dage hukuncin sai ranar 3 ga watan Fabrairu domin daya daga cikin wadanda ake kara ya rasu.
"Nine na gaba." Kamar yadda dayan wanda ake karar, Salwan Najem, ya rubuta a shafin X.
Mai shari'a wanda ke kula da karar ya ce, an kama mutane biyar dangane da kisan. Kafar watsa labarun Sweden ta SVT ta ruwaito cewa an yi kisan ne a yayin da Momika ke tsaka da amfani da TikTok, sai dai Politico ba ta iya tabbatar da hakan ba, kuma 'yan sanda ba su iya tabbatar da hakan ba.
Momika, wanda dan gudun hijira ne daga kasar Iraki wanda ya zo Sweden a shekarar 2021, ya bakanta wa dubun nan Musulmai da ke Sweden da kuma sauran kasashe rai sakamakon zanga-zangar da ya ke yi akai-akai ta nuna kiyayya ga Musulunci inda ya ke kona Al-kur'ani.
Momika ya yi gardama da cewa zanga-zangar sa a kan addinin Musulunci ne ba al'ummar Musulmi ba. 'Yan sandan Sweden sun kyale yin zanga-zangar ta shi, inda suke yin nuni da hakkin shi na fadin albarkacin baki.
An dai kona Al-kur'ani sau da dama a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2024 wanda masu kiyayya da Musulunci suka yi a Denmark da Sweden, wanda hakan ya haifar da tsaiko ga shigar Sweden kungiyar NATO. Daga karshe dai Sweden ta shiga cikin hadakar ta tsaro a watan Janairun da ya gabata.
Momiko sailin da yake yunkurin kona Alkur’ani. Yanzu dai ya koma gun Mai Alkur’anin
0 Comments