Akalla fararen hula dubu uku ne gwamnatin Jolani ta Siriya ta kashe, akasarinsu ta hanyar harbi a kusa da kusa, in ji kungiyar kare hakkin dan Adam ta ‘Syrian Observatory for Human Rights’, wata kungiyar sa ido kan yake-yake a Siriya.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon arangamar da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a tsakanin jami’an tsaron kasar Siriya magoya bayan Jolani da kuma ‘yan kasar Siriya masu adawa da gwamnatin Jolani da ke kisan mummuke wa Alawiyyawa da sauran kananan kabilu a kasar, tare da kuma kisan ramuwar gayya da ya biyo baya, ya haura sama da dubu uku ya zuwa jiya Asabar.
Wannan kisan yana daya daga cikin mummunan kisan kai a cikin shekaru goma da ya auku a Siriya, a cewar kungiyar sa ido kan yakin Siriya da ke da hedikwata a Birtaniya, SOHR.
Kungiyar ta ce baya ga fararen hula kusan dubu uku da aka kashe, akasarinsu ta hanyar harbe-harbe kusa da kusa, har wala yau an kuma kashe jami’an Jolani 125.
Masu sa ido kan yakin sun kuma kara da cewa an katse wutar lantarki da ruwan sha a manyan yankuna da ke kusa da birnin Latakia da ke gabar tekun yammacin kasar.
Rikicin dai ya barke ne a ranar Alhamis bayan kisan mummuke da sabuwar gwamnatin Siriya a karkashin Jolani ke yi wa mabiya Alawiyyawa da sauran kananan kabilun kasar, watanni uku bayan da masu tada kayar bayar suka karbe iko tare da kawar da Assad a karagar mulki.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin addinin kiristoci na kasar Siriya suka fitar sun bayyana cewa: Siriya ta sha fama da tashe-tashen hankula da cin zarafi da kashe-kashe, wanda ya haifar da kai hare-hare kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara.
Mazauna kauyuka da garuruwan da Alawiyyawa suka fi yawa sun ba da rahoton cewa ‘yan bindigar Jolani sun bude wuta kan Alawiyyah a kan tituna a yayin zanga-zangar lumana ko kuma har gida a kofar gidajensu. Kazalika wasu tarin bidiyoyi da ‘yan Siriya suka wallafa a shafukan sada zumunta na Facebook da Telegram, sun nuna yadda mayakan HTS na Jolani ke bi gida-gida suna kisan kai ga fararen hula tare da sanya wa gidajen su wuta da yi musu dauki daidai.
Garin Baniyas na daya daga cikin garuruwan da rikicin ya fi kamari. Mazauna wurin sun ce an yasar da gawawwakin daruruwa a kan tituna ko kuma an baje su a gidaje da kuma rufin gine-gine, ba tare da an samu wanda ya iya tattara su ba.
Wani mazaunin garin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, jami’an Jolani sun hana mazauna wurin kwashe gawarwakin makwabtan su guda biyar da aka kashe a ranar Juma’a na tsawon sa’o’i.
Sai dai wasu rahotanni sun kuma ce akalla mayakan HTS 16 ne aka kashe a wani arangama da aka yi ranar Alhamis din a lardin Latakia da ke gabar tekun Mediterrenean, wanda ke da al’ummar Alawiyyawa da yawa. Yankin gida ne ga sansanin sojin sama na Hmeimim - wani sansani mai dauke da kayayyakin dabarun yaki na Siriya da Rasha ke aiki da shi.
Wannan farmakin da ‘yan adawar suka yi ya zo ne bayan da a baya mai sa ido ya bayar da rahoton harin da jiragen sama masu saukar ungulu suka kaddamar a kauyen Beit’Ana da dazuzzukan da ke kewaye da kuma harin bindigogi a wani kauye da ke makwabtaka da su.
Shugabannin Alawiyyah sun yi kira a cikin wata sanarwa ta Facebook da a gudanar da zanga-zangar lumana, domin Allah-wadai da hare-haren helikwafta, wanda suka ce ana auna “gidajen fararen hula.” Sun zargi gwamnatin rikon kwarya ta Siriya ta Jolani da fifita mulki kan sake gina al'ummar kasar.
Majalisar koli ta addinin musulunci ta Alawiyyah a kasar Siriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi tir da karuwar tashe-tashen hankulan da gwamnatin kasar ke yi, da suka hada da kai hare-hare ta sama kan gidajen fararen hula da tilastawa mazauna su kauracewa gidajensu.
Sanarwar ta yi kira ga al’ummar Siriya da su gudanar da zaman dirshan na lumana tare da kauracewa barnatar da dukiya ko kuma shiga rikicin kabilanci. An ba da rahoton cewa an gwabza kazamin fada a yammacin kasar a tsakanin ragowar sojojin Larabawa na Siriya da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da kasashen yamma ke marawa baya wadanda suka shiga cikin sabuwar gwamnati ta Jolani.
Wata sanarwa da ake dangantawa ga tsohon jami’in gwamnatin Siriya Birgediya Janar Ghiath Suleiman Dalla kuma ta yadu a shafukan sada zumunta, ta sanar da kafa tare da kaddamar da “Majalisar Soji don ‘Yantar da Siriya.”
Hakan ya biyo bayan wani harin da aka kai kan dakarun gwamnatin kasar a lardin Latakia, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro sama da 10. A cewar sanarwar, manufar majalisar ita ce ‘yantar da dukkan kasar Siriya daga dukkan dakarun 'yan ta'adda masu mamaya, da kuma “gwamnatin da ke ci a yanzu tare da wargaza jami’an tsaronta azzalumai.”
Sanarwar ta yi kira ga Siriyawa daga bangarori daban-daban, yankuna, da kabilu daban-daban da su shiga cikin “sahunmu kuma su tsaya tare da mu a wannan lokaci mai cike da tarihi”.
Ta kuma bukaci al'ummomin duniya da su “goyi bayan ra'ayin mutanen Siriya na ‘yantar da kansu daga zalunci da mulkin kama karya da aka boye cikin kalmomi.”
0 Comments